Yadda Aka Gudanar Da Shagalin Bikin Jaruma Aisha Aliyu Tsamiya Cikin Sirri

Yanzu yanzu muka samu labarin yadda aka gudanar da Shagalin bikin fitatciyar tauraruwar Jaruma acikin shirin masana’antar fina-finan hausa ta kannywood jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, an gudanar da wannan Shagalin biki cikin sirri inda wasu da dama daga cikin abukan sana’ar ta basu san da faruwar wannan al’amari ba, a ranar juma’a ne jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, ta bayyana cewa za’ayi Shagalin bikin Auren ta amma sai wani watan.

Cikin mamaki kwatsam sai muka sami labari daga majiyar sirri cewa jaruma an daura mata Aure ba tare da jama’a sun sani ba cikin wadanda basu da labarin faruwar haka akwai kanin mahaifin ta wanda Tashar Tsakar Gida ta samu tattaunawa dashi inda kuma ya bayyana mata cewa shima bashida labarin faruwa haka amma ya samu labari daga baya bayan an daura.

An Daure Auren Jaruma Hafsat Idris Cikin Sirri Itama Ba’a Bayyana Ba Kamar Na Jaruma Aisha Tsamiya

An daura auren jaruma Hafsat Idris, cikin sirri kamar yadda aka daura na jaruma Aisha Tsamiya, cikin sirri duk acikin wannan sati, jaruman biyu sun Kasance jarumai masu taka tsantsan wajan kulawa da mutuncin su da kuma kimarsu cikin wannan video zakuji yadda komai ya gudana cikin tsari babu hargowa.

Sakamakon irin wannan shigar burgu da jaruman kannywood suka fara yi hakan tasa wasu na ganin cewa harkar ta fara ja baya wasu na ganin cewa suna so su tsira da mutun cin sune yasa haka duk acikin wannan video.

Sabuwar Rigima Jaruma Nafisa Abdullahi Taja Kunnen Jarumi Musa Maisana’a Kan Maganar Lalata Yam Matan Kannywood

Sabon video jan Kunnen da jaruma kuma tauraruwa acikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood jaruma Nafisa Abdullahi, inda a sati biyu da suka gabata Jarumar taja Kunnen shahararren mawakin zamani Naziru Sarkin Waka, akan irin lafazin da yayi akan cewa sai anyi lalata da yam matan cikin masana’antar kafin a sakasu cikin fina-finai su fito a matsayin jarumai.

Kwatsam sai ga bayyanar jarumi Musa Maisana’a, shima yazo yana wannan ikirari wanda yafi na mawaki Naziru Sarkin Waka, muni inda Musa Maisana’a ya sha raddi sosai daga wajan abukan sana’ar tasa yayin da jama’ar gari kuma suke yimai godiya sakamakon bayyana gaskiya tsirararta.

Wata Yar Fim Ta Tona Asiri Kafin Yasa Kani A Cikin Fim Dinsa Wallahi Sai Da Yayi Zina Dani Innalillahi Wata Yar Fim Ta Tona Asir

Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un, Allaahumma Ajirni Fil’musibati Wa’aklifni Khairan Minha. Wata jaruma cikin rashin tsoro ta fito cikin wannan video ta fadawa duniya yadda wani daraktan masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood ya yau dareta yayi zina da ita kafin ya Sakata acikin fim dinsa bayan amin ce mai ta da tayi wa’iyazubillah.

Jarumar ta bayyanawa duniya cikin wannan biyon yadda wannan darakta yayi fasikanci da ita sabuda zai Sakata acikin fim dinsa ta fito a matsayin jaruma, inda ta bayyana wasu sirri duk acikin wannan video.

Manya Manyen Malamai Sunfara Jinjinawa Jarumi Musa Mai Sana’a Akan Yadda Yake Bayyanawa Duniya Wani Sirrin Kannywood

Manya manyen malaman addinin musulunci sun fito sun fara mayar da martani akan farucin da jarumi Musa Mai Sana’a yayi akan yadda ake lalata da yara yan mata acikin masana’antar kannywood kafin a sakasu cikin fina-finai su fito a matsayin jarumai, malaman addinin musulunci sunji dadin yadda ubangiji ya fara bayyana gaskiya daga bakin abukan sana’ar tasu wa’iyazubillah, duk acikin wannan video akwai karin bayani.

Tun bayan da jarumi Musa Mai Sana’a ya fito ya gayawa duniya irin hanyoyin da yam matan cikin masana’antar kannywood suke bi wajan samun abun duniya cikin dan kan kanin lokaci yayi mutukar bawa mutane mamaki.

Manya Manyen Jaruma Kannywood Sun Shiga Cikin Tsananin Tashi Hankali Bayan Sake Bayyanar Wannan Iftila’i

Manya-manyen jaruman cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood mazan su da matan su sun shiga cikin mahuyacin hali da fargaba bayan sake bayyanar wannan mummunan al’amari, wa’iyazubillah, Jaruma Rukkayya Dawaiya ta sake bayyanawa duniya irin matsanancin tashin hankali da gori da ta sha na arziki daga wajan wasu daga cikin wayanda zakuji daga bakin ta a cikin wannan bidiyo

Jaruma cikin yanayi na rashin tsoro da salon wa’azantarwa ta sake yin wani dan tsokaci mai matukar ratsa zuciya duk acikin wannan video

Tirkashi Jaruma Rukkayya Dawaiya Ta Sake Bayyana Wani Buyayyen Sirrin Yam Matan Kannywood

Yanzu yanzu mukaci karo da wani video na fitatciyar jarumar shirin fina-finan hausa ta kannywood jaruma Rukkayya Dawaiya, inda ta ke bada wani labari mai matukar tausayi wanda ya kamata ace kowa yaga wannan video musamman yam matan cikin masana’antar fina-finan hausa ta kannywood dama sauran yan matan da basu shiga cikin wannan masana’anta ba.

Jaruma Rukkayya Dawaiya cikin yanayi na tausayi da tausaya wa ta bada wani labari cikin rashin tsoro wanda ya kamata ace ansamu wasu suna bada makamancin irin wannan kissar domin wannan babban kalubale ne ga yam mata kai harma da matan Aure wanda ke zaune acikin gidan mazajen su.

Tirkashi Jaruma Rahama Sadau Ta Sake Aikata Wani Mummunan Al’amari Hoton Batsa

Fitatciyar Jarumar shirin fina-finan hausa ta masana’antar kannywood jaruma Rahama Sadau, ta sake sakin wasu munanan hotunan ta na batsa wanda jama’a da dama suka fara yi mata raddi mai zafi akan haka sakamakon ba’a jima da jarumar ta saki wasu hutunan ta da suke nuna kusan ilahirin jikin ta.

Biyo bayan raddin da aka fara yiwa Rahama Sadau akan sakin wayen nan sababbin hutunan, ta fuskanci raddi mai zafi acikin wannan video daga wajan masoyanta maza da mata a dandalin sada zumuntar zamani.

Wanda hakan tasa jarumar mayar da martani mai zafi akan masoyan nata musamman wadan da suka ce wani abu akan wannan abun da ta aikata.

Video: Yadda Wata Mata Ta Kona Yar Kishiyarta Da Ruwan Zafi A Sokoto

Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un, yanzu yanzu mukaci karo da wani video na rashin Imani da wata mata da yiwa wata budurwa aikin rashin imani, inda ta kona mata duka ilahirin jikin ta da ruwan zafi sakamakon kiyeyya da tsananin kishi irin na mata.

Wannan yarinya mai karancin shekaru duk wani mai imanin gaske yaga wannan rashin imani, tabbas dole ya tausaya mata ya kuma yi Allah wadai da wannan mata, qalu innalillahi wa’inna ilaihiraji’un.

Idan har ya Kasance ana yiwa yaran yan matan irin wannan azaba sakamakon tsakanin kishi toh tabbas al’ummar wannan zamani bazamu zauna lafiya ba, ya kamata hukumomin kare hakkin bil’adam su shiga domin kwato mata hakkin ta tare da hukunta wannan mata.

Tirkashi Ashe Wannan Shine Dalilin Da Yasa Aka Cire Salma Kwana Casa’in Akasa Wata

Wani sabon video dake nuna sabuwar Jarumar shirin fina-finan hausa ta kannywood, mai suna Mufeeda, wadda ta kasance sabuwar jaruma acikin shirin fim din da tashar wasan fina-finan hausa ta Arewa24 ke haska fim din kwana casa’in, tun bayan dai na bayyanar tsohuwar jaruma mai suna da Salma acikin shirin, kwatsam sai aka hango wata sabuwar jaruma mai suna Mufeeda wadda ta kasance cikakkiyar mawakiyar hausa hip hop.

Daraktan shirin fim din kwana casa’in mai suna Salisu T Balarabe, daraktan yace tsohuwar jaruma Salma ita da kanta tace ta dai na fitowa acikin shirin fim din kwana casa’in, a bisa radin kanta.

Ku kalli wannan video domin ganewa kanku dalilan da suka sanya aka dakatar da jaruma Mufeeda, mai suna Salma acikin shirin kwana casa’in na Arewa24.