Yanzu yanzu muke samun wani sabon labari wanda ke bayyana mana cewa shirin fim din nan mai dogon zango na kwana casa’in ya baiyana mutuwar jaruma Salam, kwatsam ba tare da wani cikakken daliliba, amma a kwana kwanan nan munsamu wani cikakken bayani daga shafin labaran kannywood na Twitter sun baiyana cewa Salam kwana casa’in ba mutuwar gaskiya tayi ba, anyi hakan ne domin a kawar da hankalin ma’abuta kallon wannan fim mai dogon zango, duba da yadda jarumar ta ke da tarin masoya.

Jaruma Aisha Mufeeda, wadda ta kasance tana amsa sunan Salam acikin fim din kwana casa’in a matsayin yar gwamna mai suna Bawa Mai Kada, kamar yadda wasu sukayi tsammani cewa ta mutu mutuwar da babu dawowa ba haka zancen yake ba, a karshen Zango da ya gabata ne an baiyana cewa wata jaruma ta rataye kanta a cikin wani kango, inda ake zargin cewa jaruma Salman ce biyo bayan cin zarafin surukan ta wato iyayen masoyinta sahabi da mahaifiyar ta tayi ta hanyar cunu musu kare wanda hakan yasa sahabin yanke alaka da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.