Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un, yanzu yanzu wani sabon videon tonan asiri ya sake baiyana daga cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood. Tsohuwar jarumar shirin fina-finan hausa ta kannywood kuma matar margayi jarumi Ahmad S Nuhu, jaruma Safiya Musa, ta fitar da videon yadda wasu jaruman kannywood suka kashe jarumi Ahmad S Nuhu, suka yaudare shi da kudi kimanin Naira 700.

Tsohuwar jaruma Safiya Musa, cikin yanayi na tausayi da tausayawa ta baiyana yadda aka shiryo tuggu domin ganin bayan su ita da margayi Ahmad S Nuhu, jarumar bata kama sunan kowa ba amma tayi wani wankin babban bargo wanda zai sa duk wani mai cikakken hankali zai fuskanci gaskiyar al’amarin abun da ya faru acikin wannan bayani nata.

https://youtu.be/crU9-7QKIkk

Jaruma Safiya Musa, tace ankirasu ita da margiya Ahmad S Nuhu, akace za’a basu kudi masu tarin yawa inda akace ita za’a bata Naira dubu 500k shi kuma Ahmad za’a bashi Naira dubu 700k, jarumar tace ita ganin wani dalilin yasa taki kar6ar kudin ta Karbi Naira dubu 20k acikin abun da akace za’a bata, sannan kuma tace bazata je wannan tafiya da aka shirya musu ita ba, ba tare da ta baiyana dalilin yin hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.