Yanzu yanzu muka samu labarin yadda aka gudanar da Shagalin bikin fitatciyar tauraruwar Jaruma acikin shirin masana’antar fina-finan hausa ta kannywood jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, an gudanar da wannan Shagalin biki cikin sirri inda wasu da dama daga cikin abukan sana’ar ta basu san da faruwar wannan al’amari ba, a ranar juma’a ne jaruma Aisha Aliyu Tsamiya, ta bayyana cewa za’ayi Shagalin bikin Auren ta amma sai wani watan.

Cikin mamaki kwatsam sai muka sami labari daga majiyar sirri cewa jaruma an daura mata Aure ba tare da jama’a sun sani ba cikin wadanda basu da labarin faruwar haka akwai kanin mahaifin ta wanda Tashar Tsakar Gida ta samu tattaunawa dashi inda kuma ya bayyana mata cewa shima bashida labarin faruwa haka amma ya samu labari daga baya bayan an daura.

Leave a comment

Your email address will not be published.