Yanzu yanzu sabuwar takaddama ta kunno kai cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood, inda ake ta kalubalantar ‘yam matan cikin masana’antar da cewa suna bada jikin su ga maza ana lalata dasu ta bayen fage, sannan kuma sun Kasance masu gur6ata tarbiyar ‘yam matan da suka Kasance ba acikin masana’antar suke ba, amma sun dauke su abin kuyi.

Jarumin barkwanci Musa Maisana’a, ya cire tsoro a karo na biyu ya sake sakin wani sabon video da yake neman ruguza masana’antar kannywood gaba daya, inda acikin wannan sabon video da jarumi ya firta gaskiya tsirararta tun daga biri har hutsiya cikin yanayi na rashin tsoro.

Jarumi Musa Maisana’a, ya bar baya da kura tun bayan sakin wannan zazzafan video mai dauke da darasi da kuma sanin ainahin abun da wasu jarumai mata da maza suke aikatawa wajan yin fasikanci da junansu.

Leave a comment

Your email address will not be published.