Wata sabuwar kungiya ta bayyana acikin masana’antar kannywood wadda ake kyautata zaton cewa ta Mawaki Dauda Kahutu Rarara ce, kungiyar tazo da wasu sabbin abubuwa da suka tashi hankalin jama’a sosai.

Bayyanar wannan sabuwar kungiya ya sanya jama’a acikin rudani, la’akari da cewa akwai makarkashiya a tattare da wannan kungiya wadda ake so a jefa cikin zukatan al’umma da sunan kungiya.

Masu nazari akan al’amuran yau da kullum suna cewa ya kamata manazarta suyi nazari akan wannan sabuwar kungiya domin wasu matasan Arewa sun fara gangamin shiga cikin wannan kungiya ba tare da sanin manufar ita wannan kungiya da manufarta ba.

Leave a comment

Your email address will not be published.