Wata sabuwar Jaruma Ta Tona Asirin Yadda Ake Iskanci Da ‘Yam mata Acikin Kannywood.

Yanzu yanzu wani sabon video da ya tashi hankalin jarumai maza da mata har ma da daraktoci, furudusoshi na cikin masana’antar shirya fina-finan hausa ta kannywood ya sake bayyana, inda wasu gungun matasa sukayi alwashin daukar tsassauran mataki akan irin iskanci da fasikancin da akeyi acikin masana’antar tare ta kuma yadda ake zaluntar tsofaffin jarumai mata na cikin masana’antar.

Wannan sabuwar gobara da ta ke kokarin sake fullowa cikin masana’antar ta biyo bayan irin yadda wasu daga cikin jaruman masana’antar suka futo suka bayyanawa duniya yadda ake iskanci da wasu daga cikin ‘yam matan cikin masana’antar kafin a sakasu acikin fina-finai.

Bisa ga dukkan alamu wannan zance yayi matukar tada hankalin wasu daga cikin Jaruman cikin wannan masana’anta musammanĀ  yaran matan su wayanda basu san mai duniya ta ke ciki ba.

Leave a comment

Your email address will not be published.