Video: Neman Rigima, Teema Makamashi Takaiwa Sadiya Haruna Ziyara Har Prison (Gidan Gyaran Hali).

Yanzu yanzu biyo bayan hukuncin da wata kotu a jihar kano, mai zamanta akan titin filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, ta yankewa Sayyada Sadiya Haruna, hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsahon wata shida babu zabin tara, sakamakon munanan lafazai da ta yiwa jarumi Isa A Isa.

Sayyada jaruma Sadiya Haruna, ta fuskanci wani zazzafan hukunci sakamakon jifan jarumi Isa A Isa, da zargin cewa shi cikakken dan luwadi ne kuma mai fasikanci da ‘yan mata.

Tun bayan daurin da jaruma Sadiya Haruna ke fuskanta na zaman gidan gyaran hali, cikin yanayi na tausayawa jaruma Teema Makamashi, ta kaiwa Sayyada Sadiya Haruna ziyara har inda aka daureta.

Leave a comment

Your email address will not be published.